Zuwa shekara mai zuwa muna fatan Gwamnan Kano Zai Bude Makarantun Da Muka Gyara Prof Dahiru Sale Muhammed
Shugaban Hukumar kula da makarantun Kimiyya da Fasaha na jihar Kano Asso. Prof Dahiru Sale Muhammed ya bayyana cewa nan bada jimawa ba Gwamnatin jiha Kano Zata bude wasu makarantu da suka gyara a zuwan su cikin shekara daya. Babban Sakataren ya bayyana hakan ne a ranar Talatar nan yayin da yake zantawa da wasu Gidajen Jaridu a wata ziyara da suka kaimasa. Prof Dahiru yace a wannan lokaci sun dukufa wajen ganin sun farfado da Ilimin kimiyya da Fasaha a fadin Jihar Kano baki daya dan kara Bunkasa harkokin koyo da koyarwa. Dr Dahiru Sale, yace sun shirya tsaf wajen ganin sun shirya bita ta musamman ga Malaman su, wanda yace duk karshen Zango su cigaba da bada wannan bita. Gwamna Abba Kabir ya bullo da Ayukan Cigaba a fadin Jihar Kano-Hauwa Isah Sojoji Sun Kama Wani Malami Da Matarsa A Abuja “Kasancewar zamani na canzawa yake kowane lokaci yasa zamu cigaba da bada damar ba Malaman bita, wanda nan gaba zamu gayyaci manyan malaman Duniya dan su bada bita a wannan jiha tamu.. Sai dai Dr Dahir...