Zuwa shekara mai zuwa muna fatan Gwamnan Kano Zai Bude Makarantun Da Muka Gyara Prof Dahiru Sale Muhammed

Shugaban Hukumar kula da makarantun Kimiyya da Fasaha na jihar Kano Asso. Prof Dahiru Sale Muhammed ya bayyana cewa nan bada jimawa ba Gwamnatin jiha Kano Zata bude wasu makarantu da suka gyara a zuwan su cikin shekara daya.

Babban Sakataren ya bayyana hakan ne a ranar Talatar nan yayin da yake zantawa da wasu Gidajen Jaridu a wata ziyara da suka kaimasa.

Prof Dahiru yace a wannan lokaci sun dukufa wajen ganin sun farfado da Ilimin kimiyya da Fasaha a fadin Jihar Kano baki daya dan kara Bunkasa harkokin koyo da koyarwa.

Dr Dahiru Sale, yace sun shirya tsaf wajen ganin sun shirya bita ta musamman ga Malaman su, wanda yace duk karshen Zango su cigaba da bada wannan bita.

Gwamna Abba Kabir ya bullo da Ayukan Cigaba a fadin Jihar Kano-Hauwa Isah
Sojoji Sun Kama Wani Malami Da Matarsa A Abuja
“Kasancewar zamani na canzawa yake kowane lokaci yasa zamu cigaba da bada damar ba Malaman bita, wanda nan gaba zamu gayyaci manyan malaman Duniya dan su bada bita a wannan jiha tamu..

Sai dai Dr Dahiru Sale Muhammad ya koka bisa yadda ake samun Karuwar Yara marassa zuwa makaranta a cikin al’umma,inda ya kafa kwamitin gaggawa dan samun sahile masu wajen cimma Burin su na bada horo ga wadannan Yara.

” muna san kowane wata mu yaye kusan Yara kimanin dubu biyar(5000) a harkar koyar da hanyoyin dogaro dakai.”

Haka kuma ya bukaci Al’ummar jihar Kano dasu cigaba da kulawa wajen bawa ‘Ya’yan su dama wajen ilimi ta hanyar da za’a magance dukkan matsalolin da ake fuskanta.

Ya kuma ce akwai bukatar sauran Jami’an gwamnati dasu yi koyi da irin Dabi’ar mai girma gwamna Abba Kabir Yusuf wajen yadda yake kulawa da harkokin ilimi a jihar Kano.

Dahiru Sale yace tsarin da Gwamnatin Abba Kabir ta dakko domin sauya fasalin karatun kimiyya da fasaha a jihar Kano zai haifar da mai Ido.

Daga karshe yayi murna da Addu’ar fatan alkhairi ga mai girma Abba Kabir da sauran jami’an gwamnatin Kano wajen cikar gwamnatin shekara daya bisa Jagoranci na Nagari.

Comments

Popular posts from this blog

SUBEB DIGITAL PAYMENT SLIP

NUT Kano State ta magantu akan rashin sa wa wasu malamai promotion

BA ZA MU SAKE YADDA DA CIN ZARAFIN MALAMAN MAKARANTA BA