Ba Zan iya kamanta yadda naji lokacin da Gwamna yabani shugabancin KSSMB :Dr. Kabir Zakirai
Babban sakataren hukumar kula da Hukumar malaman sakandire na jihar Kano Dr. Kabir Ado Zakirai ya bayyana kudurin gwamnatin jihar Kano karkashin gwamna Abba Kabir Yusuf na kokarin dawo da martabar ilimi a jihar.
Dr. Kabir Ado ya bayyana hakane a wata zantawa da manema labarai lokacin da suka kai masa ziyarar aiki ranar Talatar nan.
Zakirai yace idan za’a iya tunawa cewa gwamna ya bayyana kudurin sa na dawo da martabar ilimi a fadin jihar Kano tun lokacin da ake yakin neman zaben da ya gabata.
Babban Sakataren ya bayyana irin koma baya da ya samu lokacin da ya samu kansa a matsayin shugaban wannan hukuma ta kula da sakandire da malamanta na jiha Kano.
Zuwa shekara mai zuwa muna fatan Gwamnan Kano Zai Bude Makarantun Da Muka Gyara Prof Dahiru Sale Muhammed
Sojoji Sun Kama Wani Malami Da Matarsa A Abuja
“Gaskiya mun sani kamar yadda kuka sani a wancan tsohuwar gwamnat an samu rashin kulawa matuka wajen abinda yashafi wannan hukuma,amma zuwa gwamna Abba Kabir ya kawo hanyoyin da ake warware wannan matsala.
Zakirai yace lallai zuwan sa wannan gurine cikin aikin gyara ilimi da gwamnan yasa gaba ya bada gudunmuwa matuka musamman duba da irin kokarin sa na inganta ilimi ya biyawa yara kudin jarabawar Weac da Neco.
Dr. Ado Kabir yaci gaba da bayyana gudanar da jarabawar karin girma na malaman ma wani abin azo aganine da gwamna yayi, tare da tsara yadda ake biyan albashin malaman makarantu ma wani abun kallone da aka samu canji na gaske.
” Akwai batun daukar malamai kimanin sama da 2000 da ya gabata kwanan baya, wanda indai mukayi duba wasu makarantun na babu malaman daga shugaban makaranta sai malami guda daya kacal.
Yace dangane da rashin malaman ne ma yasa yazuwa yanzu suka mika bukatar sake daukar malamai koda 2000 ne ga mai girma Gwamna a duk shekara idan gwamnan ya bada damar yin hakan.
“Idan mukayi duba gwamnan Kano na yanzu babu bangaren da bai taba ba wanda ya danganci kawo harkokin cigaba a jihar nan ta mu mai albarka.
Zakirai wanda ya kalli mai girma Abba Kabir a matsayin shugaba abin koyi da yabasu damar zuwa dan taimakawa al’ummar Kano kamar yadda madugu Kwankwaso yayi abaya.
Comments
Post a Comment