An rantsar da sabbin ANCOPS na kano
*ANCOPS KANO CHAPTER*
A yau ranar Talata 14/5/2024 Maigirma Kwamishinan ilimi na jahar kano Alhaji Umar Haruna Doguwa ya sa babban lauyan Ministry of Education ya rantsar da *sabbin shuwagabannin riƙo na ANCOPS Kano chapter* a Dakin taro na gidan Murtala dake ofishin Commissioner.
Maigirma Kwamishinan ilimin ya ja wa shuganin da aka rantsar kunne akan lallai su tsaya su yi aiki tukuru da kuma gaskiya. Sabanin yadda tsohuwar ANCOPS da aka sauke a dalilin yawan karɓe-karɓe da aka same su dasu , wanda shi ne dalilin sauke su kamar yadda Maigirma Kwamishinan ilimin ya bayyana a yau. Sannan ya ƙara tabbatar wa da jama'ar Kano ce wa, Gwamnatin Kano ta shirya tsaf wajan gyara makarantu da samar da kayan aiki da kuma wadatar da malamai a kowacce makaranta. Haka kuma Kwamishinan ya koka matuƙa akan yawan samun over staff da ake samu a wasu makarantun a inda ya tabbatar da wata makaranta mai Ajujuwa guda goma sha uku, amma kuma tana ɗauke da malamai sama da guda tamanin.
Comrade Auwal S. Jae@teachersmedia1452024
Comments
Post a Comment