BA ZA MU SAKE YADDA DA CIN ZARAFIN MALAMAN MAKARANTA BA
NUT KANO STATE WING
A yau Litinin 13/5/2024 Maigirma State NUT Chairman *Comrade Baffa Ibrahim Garko* ya kai ziyarar nuna jaje makarantar *GJSS Ɗanmali* akan mummunan harin da wasu iyayen yara su ka kai wa Vice principal ta makarantar a satin da ya gabata .
Maigirma Chairman ya ƙara jaddada wa al'umma jahar Kano musamman iyayen yara da sauran mutanen gari ce wa, daga yanzu ƙungiyar malaman makaranta ta NUT ba za ta sake zuba ido ba wani ko wasu mutane su ke shiga har makaranta su na cin zarafin malaman makaranta ba. Ya kuma ƙara da ce wa, duk wanda aka sake samu da aika irin wannan munanan halaye na cin zarafin malaman makaranta, to sai inda ƙarfinsa ya ƙare.
Comrade Baffa ya ƙara da ce wa, lallai malaman makaranta su tsaya su kare aikinsu yadda ya kamata. Kuma ƙun ƙungiyar NUT kofarta abuɗe ta ke wajan ganin an share wa kowanne malami hawayenshi a duk inda ya ke a duk faɗin jahar Kano.
A inda shi kuma shugaban makarantar GJSS Ɗanmali ya ce , tabbas shi a yanzu ma ya fara son aikin koyarwa a sakamakon ƙokari da nuna halin kula wa akan abun da ya samu vice principal ta GJSS Ɗanmali da kuma GGSS Zawachiki.
Shugaban NUT reshen karamar hukumar Kumbotso *Comrade Sani* ya yaba wa State NUT Chairman bisa nuna goyon bayansa da ya ke yi ga dukkanin malaman makaranta musamman na karamar hukumar Kumbotso.
Comrade Auwal S. Ja'e
@nutkano13052024
Comments
Post a Comment