SAKATAREN ILIMI NA KMC LGEA
Sakataren Ilimi na Karamar Hukumar Birni Comrade Nura Sulaiman ya bayyana cewa yana da kyakkyawan shirin na aiki kafada da kafada da shugabannin sassan na sashen ilimi da shugabannin makarantu na karamar hukumar don ganin an ciyar da ilimi gaba a fadin karamar .
Comarade Nura ya a lokacin taron da yayi da shugabannin makaranatar firamare ta a kwalli mai taken SABUWAR MUNICIPAL akan harkar ilimi inda ya shaidawa Al’umma cewar dole ne kowa ya tsaya tsayin daka akan aikinsa don kai wa ga nasara.
Sakataren ilimi ya yi kira ga shugabanin makarantu da kungiyoyin Al,umma gatan makaranta da kungiyoyin tsofaffin Dalibai da kungiyar malamai da iyayen yara da kungiyar iyaye mata, da suzo a hadu domin ciyar da ilimi gaba musamman ta fannin karfafa zuwan yara makaranta da kuma dawo da yaran da suka daina zuwa makaranta da inganta ilimin yara mata.
Comrade Nura ya hori malaman makaranta da su kara jajircewa domin inganta ilimi a karamar hukumar don bawa gwamnati kwarin gwiwa akan kudirinta na habbaka ilimi a jahar kano baki daya.
Ya nanata kudurinsa wajen ci gaba da kai ziyara makarantu don tabbatar aikin koyo da koyarwa na tafiya kamar yadda aka tsara. Inda ya bawa shugabannin makarantu damar rubuta rahoto a kan duk malamin da baya kula da aikin sa.
Akarshe yayi godiya da shubannin sassan ilimi da shugabannin makarantu bisa hadin kai da suke ba shi wajan ganin an inganta harkar koyo da koyarwa a fadin karamar hukumar burni
Comments
Post a Comment