NLC KANO TA YI WATSI DA BATUN KARIN ALBASHI

Kungiyar kwadago ta kasa NlC reshen jihar kano tayi watsi da batun Karin mafi karancin albashi da kashi 35 Cikin dari da gwamnatin tarayya ta yiwa ma;aikatan kasar nan

Da yake zantawa da wakilinmu rabiu ahmad kofar mazugal ta wayar tarho, shugaban kungiyar kungiyar na jihar kano kwamarade kabiru inuwa ya bayyana cewa kafin amincewa da duk wani Karin mafi karancin albashi akwai wasu matakai da ya kamata gwamnatin tabi

Kwamarade kabiru yace daga cikin matakan akwai samar da kwamitin hadin guiwa tsakanin gwamnatin tarayya da kuma kungiyoyin kwadago da kuma mikawa majalisar tarayya batun domin ya zama doka

Dan haka acewar kwamarade kabiru inuwa, wannan Karin da gwamnatin tarayya tayi basu gamsu dashi ba, kasancewar batabi ka;idar yadda yakamata tayi ba

Comments

Popular posts from this blog

SUBEB DIGITAL PAYMENT SLIP

BA MU YADDA DA YANKAN MORTGAGE BA- NUT

BA ZA MU SAKE YADDA DA CIN ZARAFIN MALAMAN MAKARANTA BA