KANO MAY DAY 2024 CELEBRATION
Kungiyar kwadago ta jahar Kano tare da kafatanin ƙungiyoyin da su ke ƙarƙashinta su ka gabatar da taronta na murnar zagayowar ranar ma'aikata ta Duniya (Workers Day 2024) a inda ƙungiyar malaman makaranta (NUT) ta zama zakaran gwaji a faretin gaisuwa ga maigirma mataimakin Gwamna. Wanda hakan ne ya sa aka bawa ƙungiyar NUT Babban Kofi na karramawa. Saboda kwazo da su ka nuna a wajan yin faretin girmamawa da kuma gudanar da aikin koyarwa ba tare da nuna banbanci ba wajan haɗa kan malaman makaranta da kuma bawa gwamnati shawarwari na gari.
Comrade Baffa Ibrahim Garko shugaban ƙungiyar NUT reshen jahar Kano ya nuna farin cikinsa akan wannan karramawa da aka yi wa NUT ta jahar Kano.
. NLC ta jahar Kano ta nuna ce wa, NUT ce kadai ƙungiyar malaman makaranta ta hakika wadda take ƙarƙashinta. A inda Secretary NLC ya ce , Ƙungiyar ASUSS ba ta cikin jeran ƙungiyoyin da su ke ƙarƙashin Tutar NLC ta ƙasa . Amma an gode musu tunda sun zo taron da bai shafe su ba.
Comrade Auwalu S. Ja'e
@teachersmedia@20240501
Comments
Post a Comment