Posts

Showing posts from November, 2023

NUT ta yaba wa Gwamnatin Kano

Image
Ƙungiyar malaman makaranta Reshen jahar Kano (NUT) bisa jagorancin Comrade Baffa Ibrahim Garko ta yi godiya ga Gwamnatin jahar Kano bisa dawo da sababbin malaman makaranta da aka dawo dasu bakin aiki . Haka zalika ƙungiyar ta sake yin kira ga Gwamnatin da ta yi duk maiyuwu wa wajan ganin an dawo wa da dukkanin malaman makaranta promotion da aka dakatar musu da shi.   Comrade Auwalu Shuaibu Jae     Teachersmedia@24/11/2023

Gwamnatin jahar Kano za ta dawo da ma'aikata sama da 9,332.

Image
  Gwamnatin jahar Kano ta amince da dawo da ma'aikata kimanin 9,332 daga cikin wadanda aka dakatar a watan Mayu 2023 .    Gwamnatin jahar ta ce gwamnatin da ta gabata ta dauki mutane da yawa wadanda ba su cancanta ba. Saboda a binciken da aka yi an gano har yarinya yar shekaru 13 aka ɗauka aiki .

NUT Kano sun bawa Principal na GJSS Achika ₦50,000

Image
A Ranar Asabar 11/11/2023 Ƙungiyar malaman makaranta ta jahar Kano NUT ta bawa Mal. Rabi'u gudummawar ₦50,000 domin rage masa raɗaɗin satar da aka yi masa ta Abun Hawa a gidansa dake Wudil LGA har ma da wasu da dama daga kananan hukumomin Jahar Kano.    nutkano@mediahouse

Kano State NUT chairman Comrade Baffa Ibrahim Garko ya sake isar da koken malaman makaranta wajan Gwamnan jahar Kano ta gidan Talabijin na ARTV Kano.

Image
  A ranar Laraba 8/11/2023 shugaban ƙungiyar malaman makaranta Reshen jahar Kano NUT Comrade Babba Ibrahim Garko ya sake isar da koken malaman makaranta zuwa ga His Excellency Eng Abba Kabir Yusuf da yi wa Allah ya dawo wa da Malaman makaranta promotion da aka cire musu a watannin baya . Sannan kuma ya sake kira ga Gwamnatin jahar Kano da ta yi kokari ta daidaita albashin malaman Primary daidai dana malaman Secondary. Sannan kuma ya sake isar da koken sababbin malaman makaranta da aka dakar da albashinsu domin a yi gaggawar dawo musu da shi kamar yadda aka dawo dana 'YanBESDA. Har ila yau ya sake neman taimakon gwamnati akan ta yi kokari ta waiwayi yan Deployed staff wadanda aka mayar da su hukumar KSSSMB da kuma Higher Education. Badon komai ba sai dan duba da irin halin matsin rayuwa da ake ciki.    Comrade Baffa ya yi jawabin irin Nasarorin da kungiyar NUT ta samu tun daga 2015 har izuwa wannan shekara ta 2023, a inda ya ce: Kungiyar NUT reshen jahar Kano ta yi kokarin...

Nigeria Union of Teachers Kano State Wing (NUT) ta kai wa iyalan marigayi Malam Mustapha Wada tallafin kuɗi na ₦160,000

Image
 A Ranar Litinin 6/7/2023 ƙungiyar malaman makaranta Reshen jahar Kano (NUT Kano State Wing) tare da haɗin guiwa da ƙungiyar Head Mastoci ta Dala LGEA su ka kai wa iyalan marigayi Malam Mustapha Wada tallafin kuɗaɗen ₦160,000 domin rage musu raɗaɗin rashin da aka yi. A inda Comrade Naziru ( NUT Dala Branch Chairman ya mika wa iyalan marigayi Malam Mustapha Wada waɗannan kuɗaɗe tare da yi masa addu'a ta neman rahamar Allah Subhanahu wata'ala. A inda shi kuma wakilin state NUT chairman Comrade Kabiru Fagge ( 3rd Vice Chairman) ya yi wa iyalan fatan Alkhairi tare da nuna wa iyalan cewa, state NUT a shirye ta ke kullum domin tallafawa marayun da aka bari a kullum.  Comrade Auwalu Shuaibu Mallam Ja'e ɗauke da rahoto.   Kano Teachers Media@6/7/2023