Kano State NUT chairman Comrade Baffa Ibrahim Garko ya sake isar da koken malaman makaranta wajan Gwamnan jahar Kano ta gidan Talabijin na ARTV Kano.

  A ranar Laraba 8/11/2023 shugaban ƙungiyar malaman makaranta Reshen jahar Kano NUT Comrade Babba Ibrahim Garko ya sake isar da koken malaman makaranta zuwa ga His Excellency Eng Abba Kabir Yusuf da yi wa Allah ya dawo wa da Malaman makaranta promotion da aka cire musu a watannin baya . Sannan kuma ya sake kira ga Gwamnatin jahar Kano da ta yi kokari ta daidaita albashin malaman Primary daidai dana malaman Secondary. Sannan kuma ya sake isar da koken sababbin malaman makaranta da aka dakar da albashinsu domin a yi gaggawar dawo musu da shi kamar yadda aka dawo dana 'YanBESDA. Har ila yau ya sake neman taimakon gwamnati akan ta yi kokari ta waiwayi yan Deployed staff wadanda aka mayar da su hukumar KSSSMB da kuma Higher Education. Badon komai ba sai dan duba da irin halin matsin rayuwa da ake ciki.
   Comrade Baffa ya yi jawabin irin Nasarorin da kungiyar NUT ta samu tun daga 2015 har izuwa wannan shekara ta 2023, a inda ya ce:
Kungiyar NUT reshen jahar Kano ta yi kokarin ganin an yi wa malaman makaranta na primary promotion na 2009 dana 2010 dana 2011 dana 2012 dana 2013 har izuwa 2016 a shekarar 2017. Har ila yau ya ce kungiyar NUT ce ta yi duk maiyuwuwa wajen ganin an sa wa dubban malaman Primary promotion na 2022 wanda shi ne aka cire a halin yanzu. Sannan ya sake da cewa, kungiyar NUT kullum a tsaye su ke wajan ganin an dawo da wannan promotion na malaman makaranta baki ɗaya.
  Comrade Baffa ya yi kira ga dukkanin malaman makaranta wadanda su kai karatun NCE (TUP) a FCE Kano da FCE Bichi da su kara haƙuri wajan rashin ƙarɓar NCE certificate nasu. Wanda insha Allahu nan da ba da dadewa ba za su karɓi kayansu.
  Comrade Auwalu Shuaibu Jae ɗauke da rahoto.
  Teachers Media@8/11/2023

Comments

Popular posts from this blog

SUBEB DIGITAL PAYMENT SLIP

NUT Kano State ta magantu akan rashin sa wa wasu malamai promotion

BA ZA MU SAKE YADDA DA CIN ZARAFIN MALAMAN MAKARANTA BA