Nigeria Union of Teachers Kano State Wing (NUT) ta kai wa iyalan marigayi Malam Mustapha Wada tallafin kuɗi na ₦160,000
A Ranar Litinin 6/7/2023 ƙungiyar malaman makaranta Reshen jahar Kano (NUT Kano State Wing) tare da haɗin guiwa da ƙungiyar Head Mastoci ta Dala LGEA su ka kai wa iyalan marigayi Malam Mustapha Wada tallafin kuɗaɗen ₦160,000 domin rage musu raɗaɗin rashin da aka yi. A inda Comrade Naziru ( NUT Dala Branch Chairman ya mika wa iyalan marigayi Malam Mustapha Wada waɗannan kuɗaɗe tare da yi masa addu'a ta neman rahamar Allah Subhanahu wata'ala. A inda shi kuma wakilin state NUT chairman Comrade Kabiru Fagge ( 3rd Vice Chairman) ya yi wa iyalan fatan Alkhairi tare da nuna wa iyalan cewa, state NUT a shirye ta ke kullum domin tallafawa marayun da aka bari a kullum.
Comrade Auwalu Shuaibu Mallam Ja'e ɗauke da rahoto.
Kano Teachers Media@6/7/2023
Comments
Post a Comment