Posts

NUT KANO BA TA SAN WANI ALWAILARI MEDIA PRESS BA- Comrade Auwal Shuaibu

Image
Kungiyar malaman makaranta reshen jahar Kano ta barranta kanta daga wani link mai suna Alwailari Media Press.   Shugaban ƙungiyar malaman makaranta reshen jahar Kano ta  NUT Comrade Baffa Ibrahim Garko ya ce , akwai wani link maisuna Alwailari Media Press da ake yada wa domin wai malaman makaranta su shigar da bayanansu , wanda zance ne mara tushe. Comrade Garko ya yi jan kunne ga dukkanin malaman makaranta da su kaura ce wa shiga wannan link domin kaucewa shiga cikin matsala musamman ta albashi. Comrade Garko , ya ƙara da ce wa sun yi cikakken bincike akan sahihancin shi wannan link maisuna Alwailari Media Press, wanda a binciken da aka yi shi wannan link ba shi da asali a hukumance . Dan haka malamai su guji shiga cikin shi wannan link.   Comrade Auwal Shuaibu 

PROFESSOR RAKAKA YA RASU

Image
Inna'lillahi wa'inna'ilaihirraju'un.    Professor Sani Hamisu Rakaka ya rasu .   Professor Sani Hamisu Rakaka na jami'ar Bayero ya rasu a ranar Alhamis 3/4/2025. Rakaka na daya daga cikin profesoshin sashen Nazarin Harsuna na jami'ar Bayero dake Kano a fannin Larabci (Arabic Department). Allah ya ji ƙansa da rahama. Baba Comrade dauke da rahoto daga El-magazine03042025

VERIFY YOUR PAYMENT VOUCHER BEFORE PAYMENT- Auwal Shuaibu

Image
PRESS RELEASE  19th March 2025 Kano HOS Flagg off Distribution of Salary Payment Vouchers to MDAs The Head of Civil Service Kano state, Alhaji Abdullahi Musa has today Flagg off the distribution of Salary Payment Vouchers to Permanent Secretaries for onward distribution to their respective MDAs. Represented by the Permanent Secretary AGS at the Cabinet office, Hajiya Bilkisu Shehu Maimota, the Head of Service said that the distribution of the vouchers is a step forward towards addressing the outcries of the workers affected by under and non payments of salaries in both the state and the local governments. ".. Salary payment Vouchers containing details of the workers have been printed by the state computer center and will be circulated to MDAs for verification by the affected workers" he added. He then appealed to the Permanent Secretaries to make the vouchers available for the workers in their respective MDAs that have been affected by the discrepancies to cross check and mad...

ZA A BIYA MA'AIKATA ALBASHI BAYAN KOWA YA TANTANCE ABUN DA ZA A BIYA SHI KAFIN SALLAR EIDL-EL-FITR

Image
Gwamnati za ta kafe sunayen ma'aikata da albashinsu dan kowa ya san abun da za a biya shi domin gujewar matsalar da aka fuskanta a baya- Auwal S. TMCS Media Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar wa ma’aikatan gwamnati a jihar cewa za a biya su albashinsu kafin bukukuwan Eid-el-Fitr, (idin Karamar sallah) wanda ake sa ran zai fara daga ranar 25 ga Maris. Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG), Faruk Ibrahim, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano a ranar Litinin. Wakilin mu na Kwankwasiyya Reporters, Comr Muhammad M Alasan, ya rawaito mana cewa an shirya taron manema labarai ne domin sanar da al’umma matakan da gwamnatin jiha ke dauka don gujewa matsalolin da aka fuskanta wajen biyan albashin watan Fabrairu. Yayin da yake jawabi a taron, Alhaji. Umar Faruk Ibrahim ya bayyana cewa gwamnati na sane da bukukuwan Sallah karama, da ke karatowa, kuma za ta tabbatar da biyan albashin watan Maris kafin bikin. A cewarsa, ma’aikatan gwamnati a jihar za su tabbatar da sahihanci...

FUEK TA KOMA YUSIF MAITAMA SULE FEDERAL UNIVERSITY OF EDUCATION

Image
Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya amince da sauya sunan Jami’ar Ilimi ta Tarayya da ke Kano zuwa sunan marigayi Yusuf Maitama Sule. Sanata Mai Wakiltar Kano ta Arewa Sanata Barau Jibrin ne ya nemi a sauya sunan jami'ar a ƙarshen shekarar 2024, jim kaɗan bayan da Gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya mayar wa da Jami'ar jihar sunanta na asali wato 'Northwest'. Idan za ku tuna Tsohon Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ne ya mayar da sunan jami'ar 'Northwest' mallakar Gwamnatin jihar zuwa Yusuf Maitama Sule a lokacin mulkinsa.

Mun gaji da yin funcen albashi- Auwal S

Image
Ma'aikatan jahar Kano sun koka akan yawan funce da ake musu akan albashinsu na wata-wata ba bisa ka'ida ba.   Wasu daga Ma'aikatan jahar Kano sun yi Allah wadai da yawan zaftare musu albashi da ake yi a duk wata daga cikin albashinsu ba tare da ka'ida ba. Kamar yadda wasu ma'aikata su ka sanar da manema labarai a ranar Asabar 1/3/2025 , a inda su ke ce wa, kamata yai ma a yi musu ƙari saboda halin matsi da ake ciki ba ake yi musu funce ba.   Wasu ma'aikatan da ba su yadda a fadi sunayensu ba , sun ce an yanke musu sama da Naira 33,000 wasu kuma Naira 22,000 a inda wasu kuma aka yankar musu Naira 18,000.   Mun nemi masu ruwa da tsaƙi akan wannan lamari amma abun ya ci tura.

GWAMNAN KANO YA DAKATAR DA SHUGABAN MA'AIKATAN JAHAR KANO- Auwal Shuaibu Jae

Image
Gwamnan Kano ya dakatar da mai rikon mukamin Shugaban Ma’aikatan jihar saboda zargin yanke wa Ma’aikata Albashi.