FUEK TA KOMA YUSIF MAITAMA SULE FEDERAL UNIVERSITY OF EDUCATION

Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya amince da sauya sunan Jami’ar Ilimi ta Tarayya da ke Kano zuwa sunan marigayi Yusuf Maitama Sule.

Sanata Mai Wakiltar Kano ta Arewa Sanata Barau Jibrin ne ya nemi a sauya sunan jami'ar a ƙarshen shekarar 2024, jim kaɗan bayan da Gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya mayar wa da Jami'ar jihar sunanta na asali wato 'Northwest'.

Idan za ku tuna Tsohon Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ne ya mayar da sunan jami'ar 'Northwest' mallakar Gwamnatin jihar zuwa Yusuf Maitama Sule a lokacin mulkinsa.

Comments

Popular posts from this blog

BA MU YADDA DA YANKAN MORTGAGE BA- NUT

BA ZA MU SAKE YADDA DA CIN ZARAFIN MALAMAN MAKARANTA BA

MOE Kano ta soke transfer malaman makaranta