Mun gaji da yin funcen albashi- Auwal S
Ma'aikatan jahar Kano sun koka akan yawan funce da ake musu akan albashinsu na wata-wata ba bisa ka'ida ba.
Wasu daga Ma'aikatan jahar Kano sun yi Allah wadai da yawan zaftare musu albashi da ake yi a duk wata daga cikin albashinsu ba tare da ka'ida ba. Kamar yadda wasu ma'aikata su ka sanar da manema labarai a ranar Asabar 1/3/2025 , a inda su ke ce wa, kamata yai ma a yi musu ƙari saboda halin matsi da ake ciki ba ake yi musu funce ba.
Wasu ma'aikatan da ba su yadda a fadi sunayensu ba , sun ce an yanke musu sama da Naira 33,000 wasu kuma Naira 22,000 a inda wasu kuma aka yankar musu Naira 18,000.
Mun nemi masu ruwa da tsaƙi akan wannan lamari amma abun ya ci tura.
Comments
Post a Comment