SSA GIRL CHILD EDUCATION TA GABATAR DA TARON SCHOOL'S HOME MANAGEMENT SUBJECT

Ofishin babbar mai taimakawa gwamnan Kano akan harkokin Ilimin Ya’ya mata ta shirya taron na musamman domin duba tsarin darasin koyar da tattalin gida ga dalibai mata a makarantun Sakandire na jahar Kano.

A yayin taron Hafsat Aminu Adahama Babbar mai taimakawa Gwamna Abba Kabir Yusif akan ilimin Ya’ya mata tace wajibi ne a dawo da koya ilimin tattalin gida musamman a makarantun sakandire na mata a kano, ta yadda zai taimaka musu wajan tafiyar da iyalansu.

Hafsat Adahama tace idan wannan darasi ya dawo yadda ake bukhata akwai yiwuwar za’a samu raguwar mace-macen aure a jahar Kano.

Mustapha Muktar Dangishirin Gaya
GCE Advocate gaya local govt.

Comments

Popular posts from this blog

BA MU YADDA DA YANKAN MORTGAGE BA- NUT

BA ZA MU SAKE YADDA DA CIN ZARAFIN MALAMAN MAKARANTA BA

MOE Kano ta soke transfer malaman makaranta