NECO TA SAKI SAKAMAKON EXTERNAL SSCE 2024 - Auwal S. Ja'e
Hukumar jarrabawar NECO ta saki sakamakon jarrabawar Private SSCE a yau 14/2/2025.
Hukumar jarrabawar ta ce an samu kyakkyawar nasara a wannan jarrabawar ta shekarar 2024. Shugaban hukumar Professor Dantani ya ce, kimanin kaso 67.53% cikin ɗari ne su ka samu 5 credits tare da Lissafi da Turanci.
Dantani ya ƙara da ce wa, an samu raguwar maguɗin jarrabawa a wannan karin idan aka kwatanta ta da jarrabar shekarar 2023.
Hukumar ta ce, daga yanzu kowa zai iya duba sakamakon jarrabawarsa ta yanar Gizo-gizo.
Auwal Shuaibu
Ɗauke da rahoto, teachers Media.
Comments
Post a Comment