MALAMAN MAKARANTA NA ABUJA SUN SHIGA YA JIN AIKI AKAN RASHIN BIYAN ₦70000- Auwal Shuaibu
Search
Inda Ranka
Inda Ranka
NewsMalaman Makaranta Da Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi Sun Tsunduma Yajin Aiki Published 29 minutes ago on February 13, 2025By KABIRU BASIRU FULATAN Malaman Makaranta Da Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi Sun Tsunduma Yajin Aiki A
Spread the love
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ƙungiyar malamai ta NUT-FCT da ma’aikatan ƙananan hukumomi na NULGE sun fara yajin aiki na dindin a yau Alhamis, sakamakon gazawar shugabannin ƙananan hukumomi wajen aiwatar da sabon albashi mafi ƙarancin na ₦70,000 da aka amince da shi tun Disamba 2024.
Ƙungiyoyin sun koka cewa duk da cewa sauran ma’aikatan FCT sun fara karɓar sabon albashin, an bar malaman firamare da ma’aikatan ƙananan hukumomi a baya. Sun ce sun ba shugabannin isasshen lokaci domin su cika alƙawarin da suka ɗauka amma sun kasa, don haka suka yanke shawarar ci gaba da yajin aiki har sai an biya su hakkokinsu.
Comments
Post a Comment