ILIMI- Za a soke tsarin 9-3-4 System a Nigeria.
Gwamnatin ta gabatar da sabon tsarin karatun bai daya na shekaru 12, wanda zai bai wa yara damar neman ilimin firamare da sakandare a hade.
Kafin daukar wannan mataki ana kan tsarin 6-3-3-4 wato shekaru 6 a Furamare da shekaru 3 a karamar sakandire da shekaru 3 a babbar sakandire sai kuma shekaru 4 a makarantar gaba da sakandire.
Rahotanni nacewa , gwamnatin tarayyar ta koma kan tsarin 12- 4 wato an hadewa dalibai neman Ilimi daga Furamare har sakandire.
Haka kuma, an nemi majalisar kolin kan ilimi ta kasa ta amince da shekaru 16 a matsayin mafi ƙanƙantar shekarun shiga jami’o’i a kasar nan.
Ministan ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya bayyana hakan a Abuja, yayin taron gaggawa na kwamatin kula da Ilimi na kasa
A wajen taron, an samu halartar kwamishinonin ilimi daga jihohi 36 da babban birnin tarayya (FCT), hukumomi, da kungiyoyi.
A cewar Dakta Alausa, idan an haɗa ilimin sakandare cikin ilimin bai daya, dalibai za su samu damar ci gaba da karatu ba tare da katsewa ba har zuwa shekaru 16.
Ministan ilimin ya ce sabon tsarin yana cikin sababbin hanyoyin ilimi da ake amfani da su a duniya a wannan zamanin.
Ministan ya kuma ce idan ya zamana dalibai suna shafe shekaru 12 kafin shiga jami'a, da shekaru 4 a jami'a, za su samu kwarewar sana'o'i da kirkire-kirkire kafin su kammala
Comments
Post a Comment