GWAMNATIN KATSINA ZA TA SAUKE DUK WANI PRINCIPAL DA YA FAƊI JARRABAWA


Search...
Search...
HOME
LABARAI
SIYASA
MUTANE
NEWS
KATSINA POST TV
OPINION
  Friday, 07 February, 2025 |    

Gwamnatin Katsina Ta Amince Da Cire Duka Faransifal-Faransifal Din Da Suka Fadi Jarabawa
Posted By: Sadiq Bindawa -- Friday, 07 Feb, 2025
Malamai
Gwamnatin Jihar Katsina ta amince da cire shugabannin makarantu (principals) da suka gaza samun maki 50% a jarabawar gwaji da aka shirya masu a fadin jihar.

A wata sanarwa da Alhaji Nura Katsayel, Mai Baiwa Gwamnan Jihar Katsina Shawara na Musamman kan Harkokin Ilimin Sakandare, ya fitar, ya bayyana cewa waɗanda suka fadi za a tura su zuwa wasu makarantu matsayin malamai ko kuma sassa daban-daban na ma’aikatun gwamnati da suka dace da ƙwarewarsu.

Katsayal yace aa dauki matakin ne domin inganta harkar ilimi a Jihar Katsina wanda acewar shi ilimi shine babban kudirin Gwamna Dikko Radda.

Daga nan yace wannan ya tabbatar da aniyar gwamnatin Katsina na tabbatar da cewa shugabannin makarantu sun dace da tsare-tsare na ci gaban ilimi da gwamnati ke aiwatarwa.

Katsina Post ta ruwaito cewa a Jihar Katsina, sama da shugabannin makarantu (principals) 1500 ne suka zana jarabawar gwaji da aka shirya don tantance kwarewar shugabanci da ilimi. 

Jarabawar ta biyo bayan horon kwanaki uku da aka gudanar don shugabannin makarantu da mataimakansu. Horon ya fara ne ranar Litinin, 21 ga Oktoba 2024, a cibiyoyi da dama, ciki har da FCE da shiyoyin Dutsinma, Malumfashi, Funtua, da Daura. An gudanar da jarabawar a ranar Litinin, 28 ga Oktoba 2024, a dukkan shiyoyi guda biyar na jihar.

Kwamishinar Ilimin Firamare da Sakandare ta jihar, Hajiya Zainab Musawa, ta bayyana cewa shirin horon da jarabawar an shirya su ne tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Ilimi, TESCOM, AGILE, da hukumar JAMB. Horon ya mayar da hankali kan shugabanci, dokoki, da inganta manhajar darussa, tare da jarabawa ta CBT da rubutu don tantance shugabannin makarantu.

A cewarta, an aiwatar da wannan shiri bisa umarnin Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, domin bunƙasa ilimi a jihar. Ta kuma bayyana cewa jarabawar ba domin cin mutuncin wani ba ce, sai dai don inganta shugabanci da ilimi. Duk wanda ya gaza a jarabawar zai koma matsayin malami, amma yana da damar sake jarabawar a gaba don komawa muƙaminsa idan ya cancanta.

Hajiya Zainab ta jaddada cewa shirin zai taimaka wajen inganta tsarin ilimi a jihar Katsina, kuma sakamakon jarabawar zai kasance wani muhimmin mataki wajen cimma wannan buri.

 
 
 
 
 
 


Comments

Popular posts from this blog

BA MU YADDA DA YANKAN MORTGAGE BA- NUT

BA ZA MU SAKE YADDA DA CIN ZARAFIN MALAMAN MAKARANTA BA

MOE Kano ta soke transfer malaman makaranta