Kungiyar malaman makaranta reshen jahar Kano ta yi allawadai da yankan ƙuɗaɗen da aka yi wa malaman makaranta. Ƙungiyar malaman makaranta reshen jahar Kano ta NUT bisa jagorancin Comrade Baffa Ibrahim Garko ta yi allawadai da yankarwa malaman makaranta kuɗaɗen Mortgage ba bisa ƙa'ida ba. Comrade Garko ya bayyana wa manema labarai ce wa, waɗannan kuɗaɗen da aka yankarwa malaman primary a albashin watan December na shekarar 2024 an yanke su ne ba bisa ƙa'ida ba, kuma babu sa hannunta. Garko ya ƙara da ce wa, za su yi duk maiyuwuwa wajan ganin an dawo wa da kowa ƙuɗadensu. Comrade Garko ya ƙara bayyana ce wa, shi wannan tsari na Mortgage ba a sa mutum dole , sai ma'aikaci yana so ne ake sa shi akan wannan tsari na Mortgage a bisa ƙa'ida. A ƙarshe yana bawa dukkanin malaman makaranta haƙuri akan wannan abun da ya faru. Auwalu S. Jae
Kungiyar malaman makaranta reshen jahar Kano ta barranta kanta daga wani link mai suna Alwailari Media Press. Shugaban ƙungiyar malaman makaranta reshen jahar Kano ta NUT Comrade Baffa Ibrahim Garko ya ce , akwai wani link maisuna Alwailari Media Press da ake yada wa domin wai malaman makaranta su shigar da bayanansu , wanda zance ne mara tushe. Comrade Garko ya yi jan kunne ga dukkanin malaman makaranta da su kaura ce wa shiga wannan link domin kaucewa shiga cikin matsala musamman ta albashi. Comrade Garko , ya ƙara da ce wa sun yi cikakken bincike akan sahihancin shi wannan link maisuna Alwailari Media Press, wanda a binciken da aka yi shi wannan link ba shi da asali a hukumance . Dan haka malamai su guji shiga cikin shi wannan link. Comrade Auwal Shuaibu
Gwamnati za ta kafe sunayen ma'aikata da albashinsu dan kowa ya san abun da za a biya shi domin gujewar matsalar da aka fuskanta a baya- Auwal S. TMCS Media Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar wa ma’aikatan gwamnati a jihar cewa za a biya su albashinsu kafin bukukuwan Eid-el-Fitr, (idin Karamar sallah) wanda ake sa ran zai fara daga ranar 25 ga Maris. Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG), Faruk Ibrahim, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano a ranar Litinin. Wakilin mu na Kwankwasiyya Reporters, Comr Muhammad M Alasan, ya rawaito mana cewa an shirya taron manema labarai ne domin sanar da al’umma matakan da gwamnatin jiha ke dauka don gujewa matsalolin da aka fuskanta wajen biyan albashin watan Fabrairu. Yayin da yake jawabi a taron, Alhaji. Umar Faruk Ibrahim ya bayyana cewa gwamnati na sane da bukukuwan Sallah karama, da ke karatowa, kuma za ta tabbatar da biyan albashin watan Maris kafin bikin. A cewarsa, ma’aikatan gwamnati a jihar za su tabbatar da sahihanci...
Comments
Post a Comment