AN TSINCI GAWAR ƊALIBI A CIKIN MAKARANTA- Kabiru Bashir Fulatan, Daily Trust
Rahotanni sun bayyana cewa an tsinci gawar wani dalibi mai shekaru 15 a Kwalejin Fasaha da ke Malali, Kaduna, inda ake zargin wasu ɗalibai ‘yan uwansa sun yi masa duka har lahira.
AMINIYA ta ruwaito cewa wannan lamari ya tada hankalin jama’a, musamman ganin cewa a watan Janairu ma an samu rahoton mutuwar wani dalibi a makarantar Air Force Comprehensive sakamakon hukuncin da takwarorinsa suka masa.
Matsalar cin zarafi da zaluntar dalibai a makarantu na kara ta’azzara, lamarin da ke buƙatar gaggawar daukar mataki daga hukumomi.
Matakan da Ya Kamata Gwamnati ta Ɗauka
1. Tsaurara Dokoki Kan Cin Zarafin Dalibai – Ya zama dole a samar da tsayayyen doka da ke hukunta duk wani dalibi, malami, ko ma’aikaci da aka samu da laifin cin zarafi ko zaluntar wani.
Advertisement
2. Ƙarfafa Tsaro a Makarantu – A samar da jami’an tsaro ko masu sa ido domin hana irin waɗannan cin zarafi.
3. Kafa Layukan Koka wa Gwamnati – Dalibai da iyayensu su samu damar kai ƙorafi cikin sauƙi idan ana zaluntar su.
4. Ilmantar da Dalibai da Malamai Akan Hakkokin Juna – A koyar da dalibai da malamai muhimmancin mutunta juna da illolin cin zarafi.
Advertisement
5. Taka Tsantsan Wajen Hukunta Dalibai – A tabbatar da cewa kowanne hukunci yana bisa ƙa’ida kuma yana da muradin gyara ba zalunci ba.
Wannan matsala na bukatar gaggawar daukar mataki domin hana afkuwar irin waɗannan munanan al’amura a gaba.
Advertisement
Related Topics:
Don't MissMutum 80 Sun Tsallake Rijiya Da Baya A Hadarin Jirgin Sama A Toronto
Advertisement
You may likeClick to comment
Inda Ranka
Home News Privacy Policy
© 2024 - Inda Ranka -Yakam Media Services
Comments
Post a Comment