NUT/KSSSMB PROMOTION
PRESS RELEASE
17th January, 2025
Nigeria Union of Teachers ( NUT) Kano State Wing.
Na sanar da dukkanin malaman makaranta na KSSSMB waɗanda su ka yi promotional interview na January 2025 ce wa, promotional Notification Letters ta 'yan GL8&12 ta zama ready kamar yadda NUT da hukumar KSSSMB su ka tsara domin ganin kowa ya samu Notification Lettersa cikin sauƙi kuma kan lokaci domin a yi wa kowa implementation (shigarwa) ba tare da ɓata lokaci ba .
Dan haka shugaban ƙungiyar malaman makaranta reshen jahar Kano Comrade Baffa Ibrahim Garko na sanar da dukkanin malaman secondary waɗanda abun ya shafa da su je ofishin Director Promotion and Discipline domin kowa ya karɓi tasa akan lokaci kamar yadda aka tsara.
Ƙungiyar NUT ta shirya tsaf wajan ganin an shigar wa da kowa kuɗinsa akan lokaci. Insha Allahu.
Sanarwa daga
Comrade Baffa Ibrahim Garko.
State NUT Chairman
Comments
Post a Comment