NUT KANO BA TA SAN DA MAGANAR BASHIN BATAIYA BA
*PRESS RELEASE*
12th January, 2025
*NUT Kano State Wing*
Shugaban ƙungiyar malaman makaranta reshen jahar Kano Comrade Baffa Ibrahim Garko ya na sanar da dukkanin malaman makaranta na jahar Kano ce wa, NUT ta jahar Kano ba ta da masaniya akan duk wata magana ta bawa malaman makaranta bashin da wani Kamfani mai suna *Bataiya General Enterprise LTD* ya ke sanarwa tare da gayyatar malaman makaranta zuwa taron ƙaddamarwa.
Comrade Garko ya ce , ita wannan gayyata ba ta da tushe ko asali. Dan haka ya na kira ga dukkanin malaman makaranta da su ƙaurace wa wannan gayyata.
Comrade Auwal S. Jae
*Teachersmedia/nutkano12012025*
Comments
Post a Comment