Kungiyar malaman makaranta reshen jahar Kano ta yi allawadai da yankan ƙuɗaɗen da aka yi wa malaman makaranta. Ƙungiyar malaman makaranta reshen jahar Kano ta NUT bisa jagorancin Comrade Baffa Ibrahim Garko ta yi allawadai da yankarwa malaman makaranta kuɗaɗen Mortgage ba bisa ƙa'ida ba. Comrade Garko ya bayyana wa manema labarai ce wa, waɗannan kuɗaɗen da aka yankarwa malaman primary a albashin watan December na shekarar 2024 an yanke su ne ba bisa ƙa'ida ba, kuma babu sa hannunta. Garko ya ƙara da ce wa, za su yi duk maiyuwuwa wajan ganin an dawo wa da kowa ƙuɗadensu. Comrade Garko ya ƙara bayyana ce wa, shi wannan tsari na Mortgage ba a sa mutum dole , sai ma'aikaci yana so ne ake sa shi akan wannan tsari na Mortgage a bisa ƙa'ida. A ƙarshe yana bawa dukkanin malaman makaranta haƙuri akan wannan abun da ya faru. Auwalu S. Jae
Comments
Post a Comment