MOE Kano ta soke transfer malaman makaranta
MOE ta soke dukkanin Transfer da aka yi wa malaman makaranta na KSSSMB ta ranar 12/8/2024.
Babbar sakatariyar hukumar ilimi ta jahar Kano Hajiya Kubra Imam ce ta bayyana hakan a sakamakon ce wa, ita wannan transfer ba a yi ta akan ka'ida ba . Domin Transfer ce da aka yi ta ba bisa la'akari da halin da ake ciki ba na matsatsin halin ƙunci. Sannan ta ƙara da ce wa, ba daidai ba ne ba a kwashi matan aure a cillasu wurare masu nisan gaske ba. Saboda yin hakan zai haifar da yawan fashi na malaman makaranta.
2024@jae
Comments
Post a Comment