ABUBUWA 7 DA SU KA SHAFI DOKAR TA ƁACI AKAN ILIMI
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya kafa dokar ta-baci kan harkokin ilimi a yau 8 ga watan Yunin 2024. An bayyana hakan ne a gidan gwamnatin Kano a Open Arena, inda ya bayyana irin mawuyacin halin da bangaren ilimi ke ciki da kuma bukatar gyara da saka hannun jari cikin gaggawa.
Gwamnan ya ƙudiri aniyar magance tabarbarewar ilimi a Kano, wanda ya taɓa zama abin koyi ga sauran jihohi.
Batutuwan da aka bayyana sun hada da 1- karancin kwararrun malamai,
2- Rashin isassun shirye-shiryen horaswa.
3- Rashin ababen more rayuwa a makarantu.
4- Shirin gina ɗakunan gwaje-gwaje na zamani guda 300 a makarantu 100.
5- Gina sabbin ajujuwa 1000 don rage cunkoso.
6- Sake dawo da ayyukan da aka yi watsi da su a manyan makarantu.
7- Daukar Malamai da Horar da Malamai:Daukar ƙarin malamai 10,000. Horo na lokaci-lokaci da sake horar da malamai.
Daukar a ƙalla ma’aikata 1,000 a fannin ilimi da ma’aikatan da ba masu shiga aji ba a manyan makarantu.
Zuba jari a cikin kayayyakin more rayuwa don tabbatar da isassun wuraren ilimantarwa.
@akyeducationsupport.ng
Comments
Post a Comment