Gwamnatin Jahar Kano za ta ɗauki sabbin masu gadin makarantu
Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta ɗauki ma’aikata 17,400 domin tsare makarantun firamare a faɗin jihar. Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda ya sanar da hakan a shafinsa na X, ya ce matakin wani ɓangare ne na ci gaba da aiwatar da ayyuka domin dacewa da muradin gwamnatin na dawo da ƙimar ilimi a jihar. Gwamnan ya ce ” za a ɗauki ma’aikatan ne daga kowacce ƙaramar hukuma domin su tsare sabbin azuzuwan da za a gina da kuma tabbatar da lafiya da tsaron malamai da ɗalibai”. Wannan dai na zuwa ne ‘yan awanni bayan gwamnan ya sanar da ware kuɗi fiye da naira biliyan huɗu domin gina sabbin azuzuwa a makarantun firamare da ke ƙananan hukumomi guda 44 na jihar. Makonni biyu kenan dai da gwamnan na jihar Kano, Abba Kabiru Yusuf ya ayyana dokar ta-ɓaci dangane da halin da ilimin firamare yake ciki a jihar.