A yau ranar Juma'a 19/4/2024 ƙungiyar TUC reshen jahar Kano ta rantsar da sabbin shugabanninta a inda aka rantsar da Comrade Hajiya Maryam Yahaya Musa a matsayin Chairperson kamar yadda doka ta tanada.
Kungiyar malaman makaranta reshen jahar Kano ta barranta kanta daga wani link mai suna Alwailari Media Press. Shugaban ƙungiyar malaman makaranta reshen jahar Kano ta NUT Comrade Baffa Ibrahim Garko ya ce , akwai wani link maisuna Alwailari Media Press da ake yada wa domin wai malaman makaranta su shigar da bayanansu , wanda zance ne mara tushe. Comrade Garko ya yi jan kunne ga dukkanin malaman makaranta da su kaura ce wa shiga wannan link domin kaucewa shiga cikin matsala musamman ta albashi. Comrade Garko , ya ƙara da ce wa sun yi cikakken bincike akan sahihancin shi wannan link maisuna Alwailari Media Press, wanda a binciken da aka yi shi wannan link ba shi da asali a hukumance . Dan haka malamai su guji shiga cikin shi wannan link. Comrade Auwal Shuaibu
Inna'lillahi wa'inna'ilaihirraju'un. Professor Sani Hamisu Rakaka ya rasu . Professor Sani Hamisu Rakaka na jami'ar Bayero ya rasu a ranar Alhamis 3/4/2025. Rakaka na daya daga cikin profesoshin sashen Nazarin Harsuna na jami'ar Bayero dake Kano a fannin Larabci (Arabic Department). Allah ya ji ƙansa da rahama. Baba Comrade dauke da rahoto daga El-magazine03042025
Kungiyar NUT ta Dala ta kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan marigayiya Malama Aisha Abubakar wacce na daya daga cikin malaman yankin na Dala. Shugaban ƙungiyar Comrade Yahaya Ramadan shi ya ja tawagar kai wannan ziyarar domin nuna alhini da kuma jajanta wa iyalan marigayiyar. Comrade Ramadan ya yi addu'ar Allah ya ji kan malamar tare da bada tallafin kuɗi na ₦50,000 domin taimakawa iyalanta. Comrade Auwal Shuaibu dauke da rahoto. Teachersmedia@2/5/2025.
Comments
Post a Comment