Hukumar Ilimin baidaya ta jahar Kano (SUBEB)

SUBEB KANO. 
Shugaban hukumar ilimin baidaya ta jahar Kano Alhaji Yusuf Kabir Gaya ya bada umarnin ce wa , daga yanzu an dena bada shaidar kammala karatun Primary ( *First Leaving Certificate* ).
 Haka kuma duk wata dama da shirya jarrabawa ta JSS *(BECE)* ta dawo karkashin ofishin JSS tare da hadin guiwa da KERD .
 Sannan ya kara da ce wa duk wani yunkuri na samar da wata *makaranta ta community* dole ne a samar da ita bisa dokar hukumar. 
 Haka zalinka ya kara da ce wa, duk wani sabon Head *Teachers ko Principal* dole ne a naɗa shi bisa sabuwar dokar da aka ayyana a baya. 
 Daga nan ya kara da ce wa, dukkanin ma'aikatan da su ke a LGEAs da aka maida su Aji a ranar 14/9/2023 to ya zama dole su girmama wannan posting da akai musu ko su ɗanɗana kuɗarsu. 
Sannan ya ja kunnen dukkanin ES da HOUs da su guji karɓar kuɗaɗe daga hannun malaman makaranta musamman waɗanda su ke sababbi domin buɗe File ko wani abu.
  A ƙarshe ya ya tabbatar da ce wa, Gwamnati za ta sake ɗiban sabbin malaman makaranta domin cike gurbi. 
 Kuma ya tabbatar da ce wa, matsalar Promotion da maganar yan BESDA ya ku sa zama tarihi. Comrade Auwal S. Jae
 Dauke da rahoto. Teachersmedia2024

Comments

Popular posts from this blog

SUBEB DIGITAL PAYMENT SLIP

BA MU YADDA DA YANKAN MORTGAGE BA- NUT

BA ZA MU SAKE YADDA DA CIN ZARAFIN MALAMAN MAKARANTA BA