BESDA/2023-2024 PROMOTION VERIFICATION , SUBEB KANO
NUT KANO STATE WING
Kungiyar malaman makaranta ta NUT reshen jahar Kano na ƙara sanar da dukkanin malaman makaranta ce wa, a yau ranar Litinin 15/4/2024 za a fara aiwatar da ayyukan tantance malaman BESDA wadanda za a maida su permanent staff a ƙarƙashin hukumar SUBEB ta jahar Kano bisa jagorancin the Executive Chairman na hukumar kamar yadda aka tsara.
Haka kuma duk a yau za a fara shirya sabon Brief na Promotion na shekarar 2023 da kuma 2024 tare da kuma shigar da dukkanin malaman makaranta wadanda aka tsallake a baya don ganin an bawa Kowa hakkinshi.
Shugaban kungiyar Comrade Baffa Ibrahim Garko ya ja hankalin dukkanin shuwagabannin NUT na Branches wajan ganin sun tabbatar da ganin an sa duk wanda ya cancanta a wannan Promotion Brief ba tare da an samu matsala irin ta baya ba.
A ƙarshe shugaban ya isar da sakon Barka da sallah da kuma na taaziyya ga dukkanin malaman makaranta.
Wannan saƙo ne daga Shugaban kungiyar malaman makaranta reshen jahar Kano
Comrade Baffa Ibrahim Garko.
Teachersmedia@jae.com
Comments
Post a Comment