NIGERIA UNION OF TEACHERS KANO STATE WING
A ranar Alhamis 26/10/2023 Shugaban kungiyar malaman makaranta Reshen jahar Kano (NUT) Comrade Babba Ibrahim Garko ya tabbatarwa da Teachers Media ce wa, Gwamnatin jahar Kano za ta sake bawa malaman makaranta wadanda ba su da shaidar kwarewar aikin koyarwa horo na musamman kamar yadda aka yi a shekarar 2014 . Domin sama Wa malaman takardar shaidar mafi ƙarancin koyarwa wato NCE/PGDE a ƙarƙashin hukumar ilimin baidaya ta Kano wato SUBEB.
Kuma ya kara tabbatar mana da ce wa , wadanda su ka yi wancan karatu na farko a FCE Kano FCE Bichi su ma nan da bada dadewa ba za su karbi certificate na su kamar yadda takwarorinsu na LEGAL da SRCOE su ka karbi shaidarsu
Comrade Auwalu Shuaibu Jae
Dauke da rahoto.
Comments
Post a Comment