LITATTAFAN DA DANA YANZU A MAKARANTUMMU

Da za a dawo kan wannan tsohon tsarin da an samu gyaran ilimi ta fuskar iya karatu da rubutu da kuma sanin fannukan kimiyya da fasaha a dukkanin makarantunmu.
  Amma a yanzu kuma akan tsarin da ake kai sai yaro ya yi Degree amma wallahi bai iya karatu da rubutu na Harshen Hausa ba. Balle ya san al'adun Hausawa na gargajiya.
  Daina amfani da wannan tsari na Da , na ɗaya daga cikin tubalin tokar da su ka lalata darajar ilimi musamman a ƙasar Hausa.
 Idan mu kai duba akan litattafan Da irin su :-
1- Ruwan bagaja
2- Shehu Umar
3- Magana jari
4- Wasanni da al'adu
5- Iliya ɗanmaiƙarfi
6- Dodanniya maibishiya
7- Tatsuniyoyi da wasanni
8- Ka koyi karatu d.s
  Duk waɗannan litattafai su na koyar da Tarbiyya da ladabi da biyayya da raya al'adun Hausawa da kuma koyar da karatu da rubutun Hausa .
   To amma yanzu an watsar da su an kama na ƙarya. 
  Allah ya kyauta
 Comrade Auwalu Shuaibu Jae

Comments

Popular posts from this blog

SUBEB DIGITAL PAYMENT SLIP

BA MU YADDA DA YANKAN MORTGAGE BA- NUT

BA ZA MU SAKE YADDA DA CIN ZARAFIN MALAMAN MAKARANTA BA