Posts

Showing posts from April, 2025

NUT KANO BA TA SAN WANI ALWAILARI MEDIA PRESS BA- Comrade Auwal Shuaibu

Image
Kungiyar malaman makaranta reshen jahar Kano ta barranta kanta daga wani link mai suna Alwailari Media Press.   Shugaban ƙungiyar malaman makaranta reshen jahar Kano ta  NUT Comrade Baffa Ibrahim Garko ya ce , akwai wani link maisuna Alwailari Media Press da ake yada wa domin wai malaman makaranta su shigar da bayanansu , wanda zance ne mara tushe. Comrade Garko ya yi jan kunne ga dukkanin malaman makaranta da su kaura ce wa shiga wannan link domin kaucewa shiga cikin matsala musamman ta albashi. Comrade Garko , ya ƙara da ce wa sun yi cikakken bincike akan sahihancin shi wannan link maisuna Alwailari Media Press, wanda a binciken da aka yi shi wannan link ba shi da asali a hukumance . Dan haka malamai su guji shiga cikin shi wannan link.   Comrade Auwal Shuaibu 

PROFESSOR RAKAKA YA RASU

Image
Inna'lillahi wa'inna'ilaihirraju'un.    Professor Sani Hamisu Rakaka ya rasu .   Professor Sani Hamisu Rakaka na jami'ar Bayero ya rasu a ranar Alhamis 3/4/2025. Rakaka na daya daga cikin profesoshin sashen Nazarin Harsuna na jami'ar Bayero dake Kano a fannin Larabci (Arabic Department). Allah ya ji ƙansa da rahama. Baba Comrade dauke da rahoto daga El-magazine03042025