Posts

Showing posts from December, 2024

BA MU YADDA DA YANKAN MORTGAGE BA- NUT

Image
Kungiyar malaman makaranta reshen jahar Kano ta yi allawadai da yankan ƙuɗaɗen da aka yi wa malaman makaranta.   Ƙungiyar malaman makaranta reshen jahar Kano ta NUT bisa jagorancin Comrade Baffa Ibrahim Garko ta yi allawadai da yankarwa malaman makaranta kuɗaɗen Mortgage ba bisa ƙa'ida ba. Comrade Garko ya bayyana wa manema labarai ce wa, waɗannan kuɗaɗen da aka yankarwa malaman primary a albashin watan December na shekarar 2024 an yanke su ne ba bisa ƙa'ida ba, kuma babu sa hannunta. Garko ya ƙara da ce wa, za su yi duk maiyuwuwa wajan ganin an dawo wa da kowa ƙuɗadensu.  Comrade Garko ya ƙara bayyana ce wa, shi wannan tsari na Mortgage ba a sa mutum dole , sai ma'aikaci yana so ne ake sa shi akan wannan tsari na Mortgage a bisa ƙa'ida.  A ƙarshe yana bawa dukkanin malaman makaranta haƙuri akan wannan abun da ya faru.  Auwalu S. Jae

HONOURABLE RABIU SALEH GWARZO YA ZAMA SABON SHUGABAN GIDAN MALAMAI

Image
Mai girma Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya naɗa tsohon Permanent Member Honourable Rabiu Saleh Gwarzo a matsayin babban sakataren Hukumar Kula da manyan makarantun Sakandire na jahar Kano (KSSSMB) . A inda shi kuma Dr. Kabiru Ado Zakirai ya koma da aiki Kano State Library a matsayin Babban sakatare na hukumar.   Sanarwa daga babban maimagana da yawun Gwamnan jahar Kano Honourable Sunusi Bature Dawakin-tofa.   Comrade Auwal Shuaibu Jae Ɗauke da rahoto. teachersmedia@15/12/2024