NUT Kano State ta magantu akan rashin sa wa wasu malamai promotion
Kungiyar Malaman Makaranta reshen jahar Kano ta magantu akan rashin sawa wasu malaman makaranta kudin promotion wadanda su ka hau matakin albashi na GL13-GL15. Shugaban Malaman Makaranta reshen jahar Kano Comrade Baffa Ibrahim Garko ya ce, kungiyar Malaman Makaranta ba ta ji dadin rashin sa wa wasu malaman Primary Promotion da aka janye musu ba. A inda ya Kara da cewa , kungiyar ba ta San dalilin abun da jawo Hakan ba. Amma idan Allah ya Kai mu ranar Talata 2/1/2023 za su bi kadin wannan al'amari domin shawo kan matsala. Sannan ya Kara da ba wa malamai hakuri akan wannan rashin sa musu kudadensu na promotion. Comrade Auwalu Shuaibu Jae Dauke da rahoto@teachersmedia.com