NUT DALA TA KAI WA IYALAN M. AISHA TALLAFI- COMRADE AUWAL S
Kungiyar NUT ta Dala ta kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan marigayiya Malama Aisha Abubakar wacce na daya daga cikin malaman yankin na Dala. Shugaban ƙungiyar Comrade Yahaya Ramadan shi ya ja tawagar kai wannan ziyarar domin nuna alhini da kuma jajanta wa iyalan marigayiyar. Comrade Ramadan ya yi addu'ar Allah ya ji kan malamar tare da bada tallafin kuɗi na ₦50,000 domin taimakawa iyalanta. Comrade Auwal Shuaibu dauke da rahoto. Teachersmedia@2/5/2025.